Kwamishinoni: Majalisar Kano ta Amincewa Abba Gida-gida ya nada mutane 17 cikin 19 da ya tura mata

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da mutane 17 cikin 19 da gwamnan kano ya tura musu don nada su a mukaman kwamishinoni kuma yan majalisar zartarwa ta jiha .

 

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar Talata ne gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya aikewa majalisar sunayen mutane 19 da yake so majalisar ta tantance don nada su kwamishinoni.

Za mu samar da sabbin wuraren kasuwanci a Kano don rage cunkoso a birnin jihar – Abba Gida-gida

A ranar jiya Laraba majalisar ta fara aikin tantancewa, yanzu da ta tantance mutane 16 tare da amincewa dasu a Alhamis din nan.

Danbilki Kwamanda ya Koka da matakin da yace gwamnatin Kano ta ɗauka akansa

Cikin mutane 19 dai akwai mutum biyu da suka tafi aikin hajji wanda hakan yasa ba a tantance su ba sai kuma mataimakin gwamnan Kano wanda aka amince dashi ba tare da ya halarci tantamcewar ba.

Shugaban majalisar Alhaji Isma’il Falgore ya ce sun amincewa gwamnan ya nada mutanenne, bayan da shugaban masu rinjaye na majalisarmajalisar Lawan Usaini Dala ya gabatar da kuɗirin hakan, daga bisani bayan tattaunawa akan batun aka amince .

Tallah

Wadanda aka tantance kuma aka amince da su sun hadar da Hon. Umar Haruna Doguwa, Ali Haruna Makoda, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, Danjuma Mahmud, Musa sulaiman Shanono, Abbas Sani Abbas, Ladidi Garko, Marwan Ahmad, Muhd Diggol.

Sauran sune Adamu Aliyu Kibiya, Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata, Safiyanu Hamza, Tajuddeen Othman Ungogo, Nasiru Sule Garo, Barr. Haruna Isa Dederi da kuma Baba Halilu Dantiye.

Majalisa ta kuma kafa kwamiti da zai jagoranci fitar da kwamitocin majalisar na bangarori daban-daban wanda shugaban majalisar zai jagoranci kwamitin .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...