Babbar Sallah: Ma’aikatar Ilimi ta jihar kano a Amincewa dalibai su yi hutun mako guda

Date:

Daga Aisha Muhammad Adam

 

Ma’aikatar Ilimi ta jihar kano ta bada hutun mako guda ga daliban makarantu a jihar, saboda bukukuwan Sallah babba.

 

Daraktan kula da wayar da jama’a Aliyu Yusuf ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikowa kadaura24.

Ba zamu lamunci yan kama wuri zauna su cigaba da zama a Gidajen yan fansho ba – Habu Muhd Fagge

” Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta amince daga ranar Juma’a 23 ga watan Yuni 2023 a matsayin ranar da za a fara hutun Sallah babba ga daliban makarantun firamare da sakandire a jihar Kano”.

Danbilki Kwamanda ya Koka da matakin da yace gwamnatin Kano ta ɗauka akansa

Sanarwar ta bukaci Iyaye/Masu kula da dalibai da su je makarantun ya’yan su na kwana a safiyar juma’ar nan domin mayar da su Gidajen su”.

 

Hutun Sallah wanda zai dauki tsawon mako daya zai kare a Asabar 1 ga Yuli, 2023, don haka dukkan daliban makarantun kwana za su koma ranar Lahadi 2 ga watan Yuli yayin da wadanda ke makarantun jeka ka dawo za su koma ranar Litinin 3 ga Yuli. 2023 .

Tallah

Babban sakataren ma’aikatar, Malam Ahmad Tijjani Abdullahi ya bukaci iyaye/Masu kula da dalibai da daliban makarantun da su tabbatar da bin ka’idojin da aka amince da su na komawa aiki.

 

Yayin da yake yi masu fatan gudanar da bukukuwan Sallah lafiya tun da wuri, ya kuma yi kira gare su da su kasance masu taimakawa iyayensu da kuma guje wa yawon da Babu gaira babu dalili a yayin hutun Sallah.

 

Sanarwar ta kara da cewa Babban Sakataren ma’aikatar, ya kuma yi gargadin cewa za su dauki matakin ladabtarwa a kan daliban da suka gaza komawa makarantunsu akan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...