Daga Kamal Yahaya Zakaria
Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin samar da kyakyawan wakilcin na ‘yan kasuwar jihar a majalisar zartarwa ta Kano.
Ya kuma ba su tabbacin kwamishinan kasuwanci da sauran mukamai da suka danganci yan kasuwa za su fito daga cikinsu don su sami wakilci a gwamnatinsa.
Danbilki Kwamanda ya Koka da matakin da yace gwamnatin Kano ta ɗauka akansa
A sanarwar da mukaddashin mai magana da yawun gwamnan kano Hisham Habib ya aikowa kadaura24, yace Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan kasuwar Kano a gidan gwamnatin jihar.

Ya ce gwamnatinsa za ta bunkasa harkokin kasuwanci a jihar, ya kuma tabbatar wa ‘yan kasuwar kudirinsa na tallafa wa harkokin kasuwanci dai-dai da zamani.
Matakin da gwamnan kano ya dauka akan albashin ma’aikatan abun a yaba ne – Anas Abba Dala
Gwamnan ya kuma shaidawa ‘yan kasuwar shirin sa na sake fasalin kasuwannin Kano tare da tafiya kowa da bai daga .
Ya ce gwamnati za ta kuma rage cunkoso a birnin kano, ta hanyar bude sabbin wuraren kasuwanci, ya kuma bukaci matasan ‘yan kasuwa da su yi amfani da damar wajen bada hadin kai don cigaban jihar kano.
A jawabinsa Mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam, ya jaddada kokarin gwamnati na ganin an dakile matsalar cin hanci da rashawa da jami’an hukumar kula da ababen hawa ta jihar da aka fi sani da KAROTA ke yi wadanda a zamanin gwamnatin da ta shude suka yi kaurin suna wajen karbar kudi a hannun yan kasuwar.