Matakin da gwamnan kano ya dauka akan albashin ma’aikatan abun a yaba ne – Anas Abba Dala

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon Gwamnan Kano Hon. Anas Abba Dala ya yabawa gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda matakin dakatar da yankar albashin ma’aikatan Kano.

 

” Abun da ma’aikatan jihar Kano suka dade suna jira kenan tsahon shekaru 8 da suka gabata, Amma abun yaki yiwuwa sai da Abba Gida-gida ya zo don haka dole a yaba masa akan wannan mataki”.

Da dumi-dumi: Shekarau ya Magantu kan gayyatar da Majalisar Dinkin duniya ta yi masa

Hon. Anas Abba Dala ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da wakilin Kadaura24 a Kano.

Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya Magantu kan baiwa dansa mukami

Hon. Anas Dala ya ce wanna matakin da gwamnan ya dauka ya tabbatar da cewa yana kishin ma’aikatan Kano, kuma yana sane da halin da suke ciki, kuma zai cigaba da warware matsalolinsu da kuma kyautata musu.

Tallah

” A baya dai ma’aikatan sun jima suna kokawa da yadda gwamnatin baya ta rika yanke musu albashi, ta yadda da yawan ma’aikatan Kano basu san takamaiman albashinsu ba, Amma da wannan mataki na yi Imani matsalar can ta yanke-yanken albashinsu ta zo ƙarshe”. A cewar Anas Abba Dala

Ya kuma bukaci ma’aikatan jihar kano da su sakawa gwamnatin jihar kano da bata goyon baya, da kuma rubanya kokarinsu wajen aikin su don cigaban jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...