Zamu bibiyi Shari’ar Abduljabbar har Karshe – Ganduje

Date:

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bada tabbacin gwamnatin Kano zata cigaba bibiyar shari’ar Sheikh Abduljabar Nasiru kabara har zuwa Karshen ta.

Gwamnan ya bayyana hakan ne Yayin daya kaiwa Khalifan Kadiriyya na Africa Sheikh Karibullah Nasiru Kabara Ziyarar Barka da Sallah a gidansa Dake Unguwar Kabara.

Gwamna Ganduje yace kamar yadda Malamai Suka sauke Nauyinsu Kan zargin da ake yiwa Abduljabbar a Yayin muƙabala, itama gwamnati zata cigaba da bibiyar shari’ar har zuwa Karshenta.

“Ana ta cewa ga sa nan kowa ya tsaya domin yaga San Sai da aka Gama jira sai aka ga Ashe Dan akuya ne to Kun ga ba Abun daya kamata muyi Masa sai mu yanka Dan akuyan.” Inji Ganduje

Ganduje ya bayan ya yiwa Malamin Barka da Sallah ya Kuma yi alkawarin Zai cigaba da dauka matakan kariya ga fiyayyen Halitta Annabi Muhammad S A W a Matsayinsa na Gwamna tare da cigaba da karbar shawarwarin Malamai.

A Jawabinsa tun da fari Khalifan Kadiriyya na Africa Sheikh Karibullah Nasiru kabara ya godewa gwamnan da Yan tawagarsa bisa ga Zumuncin da suka sada tare da yabon Matakin da Gwamnan ya Dauka akan Abduljabbar.

“Mun ji Dadin Matakin da ka dauka na Kare Martabar ma’aiki (S A W) Wannan ta nuna kaunar ka ga Annabi Muhammad S A W mun ji Dadin mun sosai Allah ya saka maka da alkhairi.” Inji Sheikh Karibullah

“Ka Dade kana yiwa Gidan Nan hidima Kuma duk Cikin Gwamnonin da akai a Kano ba Wanda ya ajiye Lokaci irin Wannan na Sallah yake Ziyarci Wannan gida sai Kai , Suma Sauran Suna zuwa Amma ba kamarka ba.” Inji shi

Sheikh Karibullah ya bukaci Gwamnan daya taimaka musu wajen basu Gudunmawa don kammala Aikin Cibiyar Sheikh Nasiru Kabara ta Kasa dake Abuja.

Gwamna Ganduje ya Kai Ziyarar Barka da Sallah ga iyalan Marigayi Dan Masanin Kano da Iyalan Marigayi Sheikh Isyaka Rabi’u da Hajiya Mariya Sunusi Dantata da Musa Gwadabe da dai Sauran muhimman Mutane a Kano.

298 COMMENTS

  1. Kaji wane wasan yara gsky kun raina yan kano wlh kun mayar da mutane sai kace wasu yan kwallo kaji wata mgn mara amfane gsky ya kmt wannan tsohon ku kaishe ?

  2. Усик – Джошуа – Все Последние Новости Онлайн Джошуа Усик смотреть онлайн Британця турбує той факт, що українець є лівшею. Чемпіон WBA, IBF, WBO і IBO в суперважкій вазі Ентоні Джошуа (24-1, 22 КО) назвав головну перевагу свого опонента в майбутньому поєдинку – українця Олександра Усика (18-0, 13 KO

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...