Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya umurci dukkan wadanda aka tura sunayen su domin nada su a matsayin kwamishinoni da su tabbatar sun bayyana abubun da suka mallaka ga hukumar kula da da’a ma’aikata ta kasa.
“Ana sa ran wadanda aka zaba za su bayyana kadarorinsu a cikin mafi kyawun lokaci kafin a fara tantance su a majalisar dokokin jihar a ranar Alhamis 22 ga watan Yuni, 2023 da karfe 10 na safe a harabar majalisar dokokin jihar”.
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya Magantu kan baiwa dansa mukami
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.
Matakin da gwamnan kano ya dauka akan albashin ma’aikatan abun a yaba ne – Anas Abba Dala
Gwamnan ya sha alwashin babu wani kwamishina da za a rantsar da shi a matsayin memba na majalisar zartarwa ta jihar kano ba tare da ya cike fom din bayyana kadarorinsa ga hukumar kula da Da’ar Ma’aikata ba.
“Duk sauran masu rike da mukaman siyasa a karkashin wannan gwamnati su ma za su bi wannan umarnin .”

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada aniyarsa ga mutanen jihar Kano na gudanar da komai a bayyane kamar yadda yake cikin manufofin da ya bayyana yayin yaƙin neman zaɓen 2023.