Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya musanta labarin da ake yadawa cewa ya nada dansa a matsayin Sakataren zartarwar na hukumar Adana tarihi da al’adu ta jiha .
Idan za’a iya tunawa wasu jaridu sun rawaito Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa ɗansa na riƙo, Ahmad A. Yusuf a matsayin Sakataren zartarwar na Hukumar Tarihi da Al’adu ta jihar.
Yanzu-Yanzu: Abba Gida-gida ya tura sunayen wadanda zai nada a matsayin kwamishinoni
Rahotan dai ya bayyana cewa Ahmad A. Yusuf ɗa ne ga shaƙiƙin gwamnan, amma a hannunsa ya taso har ma ake masa kallon ɗansa na fari.
Da dumi-dumi: Shekarau ya Magantu kan gayyatar da Majalisar Dinkin duniya ta yi masa
A wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, yace Art. Ahmad Abba Yusuf da ne ga Sakataren Masarautar kano Alhaji Abba Yusuf.
Idan za a iya tunawa dai, lokacin da gwamnan ke karɓar satifiket na nasarar zaɓensa daga hukumar zaɓe, INEC ranar 29 ga Maris, 2023, gwamnan ya bada tabbacin cewa ba zai sa iyalinsa cikin harkokin mulki ba.
Babu yadda za a yi in bar iyalina su tsoma baki a harkokin gwamnati ba, saboda ni kaɗai na rantse ba tare da su ba, wato dai su babu su a gwamnati,’” in ji Gwamnan.