Daga Rahama Umar Kwaru
Yanzu haka dai tsohon gwamnan jihar Benue Samuel Ortom yana hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gayyaci tsohon gwamnan domin amsa wasu tambayoyi dangane da mukamin gwamna da ya rike.
Yanzu-Yanzu: Abba Gida-gida ya tura sunayen wadanda zai nada a matsayin kwamishinoni
Ortom, ya shiga ofishin hukumar na shiyyar Makurdi, wanda ke kan titin Alor Gordon a babban birnin jihar da misalin karfe 10:08 na safe.

Kai tsaye ya shiga cikin ginin.
Daily trust ta ruwaito yadda Ortom ya mika bayanan bashi na Naira biliyan 187.7 ga gwamnatin Reverend Father Hyacinth Alia.