Kungiyar Agaji Tara kasa reshen jahar Kano ta yabawa Gwamnatin jahar Kano bisa girmama addinin musulunci da malamai da takeye.
Shugaban kungiyar na jahar Kano Muhd Nuruddeen Lawan Gwagwarwa ne ya baiyana haka a sakonsa na barka da sallah ga al’ummar musulmi.
Yace gwamnatin jihar Kano tayi abun a yaba Mata Saboda da Matakin data dauka akan Wani Malami da yasu Kawo rudani da raba Kan mabiya addinin Musulunci.
Yace Yana Taya daukacin al’ummar musulmi Kano Dana Nigeria Baki daya Murnar zagayowar idin Babbar Sallah, Inda ya bukaci al’umma su cigaba da yin koyi da aiyukan alkhairin da Suka gabatar a kwanaki 10 Farko na Watan zulhijja.
Alhaji Nuruddeen Gwagwarwa ya Kuma yabawa malamai bisa addu’o’i da ilimantarwa da wayar dakan al’umma da suke akoyaushe, Sannan yayi kira ga al’ummar musulmi dasu kasance masu bin tsarin shari’ar musulunci a dukkan lamuransu na yau da kullun.
Shugaban Kungiyar ya Kuma yi kira ga Malamai a jihar nan dasu karfafa tsarin hadinkai, fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin alumma’a. A kashe ya Kuma yi kira ga al’umma dasu cigaba da adu’o’in samun zaman lafiya Mai dorewa a Kano da Kasa baki daya