Marayu 100 a kano sun rabauta da Tallafin Naman Sallah daga Falakin Shinkafi

Date:

 

Kimanin Marayu 100 sun Amfana da tallafin Naman Sallah da Barka da Sallah a unguwar Yakasai Daga Wani Dan Kasuwa Kuma Dan kishin Kasa Ambasada Yunusa Yusuf Hamza ( Falakin Shinkafi).

Da yake Zantawa da Wakilin Kadaura24 Jim kadan bayan kammala rabon Falakin Shinkafin Amb. Yunusa Yusuf yace ya tallafawa marayun ne domin Sanya farin Ciki a zukatansu a Wannan Lokaci na Sallah Babba.

Yace Marayu Suma’ya’yane da ya kamata a Rika kula dasu Musamman a Lokaci irin Wannan domin a dauke musu radadin Rashin Iyayen su.

Amb. Yunusa Yusuf yace ya Zama wajibi mawadata su Rika tallafawa marayu don kyautata Rayuwar su, “Idan ba’a taimaki Rayuwar su ba hakan ce take sawa su taso basa tausayi Kuma su zamo gurbatattu Saboda da Suma ba’a taimaki Rayuwar suba.

” Ina Amfani da Wannan dama wajen Kira ga Shugabanni da mawadata dasu Rika tallafawa marayu don inganta Rayuwar tare da Samun lada Mai yawa a wajen Allah”. Inji Falakin Shinkafin

Wasu Daga Cikin Iyayen Marayun da Suka Amfana da tallafin sun yabawa Ambassador Yunusa Yusuf Hamza (Falakin Shinkafin) bisa tallafin da ya Baiwa ya’yansu, Inda Suka ce dama ya saba gudanar da irin Wannan tallafi ta karkashin Kungiyar Yakasai Zumunta.

Kadaura24 ta rawaito bayan Naman Sallah Marayun sun rabauta da kudi da Kayan more Rayuwa don faranta musu a Wannan Lokaci na Sallah.

98 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An sanya dokar hana fita a Jigawa

An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare...

Gwamnan Kano ya bayyana abun da gwamnatin za ta yi a filin Idi

  Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar...

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...