Ya kamata sabbin gwamnatoci su maida hankali don sauke alkawarun da sukai – Musa Muhd Alto

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama

 

Kungiyar dake fafutukar ganin matasan Najeriya sun samu ayyukan yi ta kasa, ta shawarci gwamnatin tarayya da ta jihar kano, da su lalubo hanyoyin sauke nauyin alkawaran da suka dauka a lokacin da suke yakin neman zabe.

Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji musa Muhammad Alto,Wanda aka fi sani da Blue Line ne ya ba da shawarar a yayin da kungiyar ta gudanar da taron manema labarai a ofishinsa dake nan kano.

Muhammad Alto yace kungiyar tayi duba da halin da matasan Arewacin Najeriya suke ciki na rashin ayyukan yi, wanda rashin ayyukan yi na daya daga cikin abubuwan da suke jefa matasa maza da mata harkar shaye-shaye da kwacen waya da sauran aiyukan ta’addanci.

Yace tun yanzu ya kamata Gwamnatoci su yi duk mai yiyuwa wajen cika alkawarin da suka yiwa al’umma musamman matasa.

Shugaban yayi kira ga sabon shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da yayi duba akan cire tallafin man fetur da yayi, wanda hakan zai jefa al’ummar kasar nan cikin wahala, musamman wajen hau hawar farashin kayan masarufi wanda akasari yana karewane akan Talakawan kasar nan.

“Idan har dole ne gwamnatin tarayya sai ta cire Tallafin man fetur din, to ya kamata ta bijiro da wasu hanyoyin magance hauhawar farashin kayayyakin, kasancewar akwai hanyoyi da dama da gwamnatin take da su wajen magance wannan matsala, tun da gwamnati uwar kowace”. Inji Muhammad Alto

Muhammad Alto ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf da ta bashi dama a matsayinsa na kwararren injiniya domin ba da tashi gudunmawar wajen Samar da ruwan sha a fadin jihar kano da hasken wutar lantarki.

“Akwai hanyoyin da masana a kasashen Duniya suke amfani da su wajen magance matsalolin rashin ruwan sha da wutar lantarki, kadan daga cikin wasu hanyoyin da ake Samar da su, ta hanyar kafa shigayen bincike, wato(Toitleget)Hayace da take Samar da kudaden shiga Gwamnati da yin amfani da su wajen yiwa alumma kasa ayyukan da kuma, Samar musu da ayyukan yi batare sai sun yi aikin Gwamnati ba”.

Shugaban kungiyar yace wannan kungiya da suka kafa akwai kwararrun matasa da suka yi zurfi wajen kafa kamfanoni na sarrafa kayayyakin cikin gida da ya kamata Gwamnatin jihar kano, ta zauna da su domin ba da ta su gudunmawar da jin irin fasahar Allah ya basu.

Shugaban ya bayyana cewa, ‘Ya’yan kungiyar sun yi tattaki zuwa kasashen ketare domin Neman ilimin Samar da sana,oin dogaro da kai da sanin makamar aiki musamman na kamfanoni da masana,antu da sai saurasu.

A cewarsa,wannan dama ce ga sabuwar wannan Gwamnati da ta yi amfani da wannan dama ta hada hannu da hukumar gudanarwar wannan kungiya wajen magance matsalolin rashin ayyukan yi a fadin jihar kano duba da halin da mayasa suke ciki a yanzu na harkokin shan muggun kwayoyi da kwacen wayoyi Wanda rashin ayyukan yi da rashin ilimin islamiyya Dana Boko suke haifar da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...