Rasuwar Mahaifiya ga Sarakunan Kano da Bichi, Babban Rashi ne ga Kasa- Garban Kauye

Date:

Daga Surayya Abdullahi Tukuntawa

Shugaban karamar Hukumar Kumbotso Hon Hassan Garban Kauye Farawa ya Bayyana Rasuwar Hajiya Maryam Ado Bayero ( Mama Ode ) Mahaifiyya ga Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero Dana Bichi Alh Nasir Ado Bayero amatsayin Babban Rashi ga Kasar Nan Baki Daya Ba iya jihar Kano ba.

Shugaban karamar Hukumar ta Kumbotso Alh Hassan Garba Amadadin Al’ummar karamar hukumar ta Kumbotso na Mika Sakon Ta’azziya ga Masarautar Kano Da Bichi da Kuma Mai girma gwamnan jihar Kano Dr AU Ganduje, Shugaban jam’iyar APC Hon Abdullahi Abbas Sunusi, kwamishinan kananan Hukumomi Hon Murtala Sule Garo da Daukacin Al’ummar jihar Kano. da fatan Allah Swt ya Kai Rahama kabarinta.

” Innalillahi wa innailahir raji’un Allah Daya Dauketa yafimu Sonta, Allah ya Bata Albarkacin Wannan wata na Ramadan ya garfarta Mata” a cewarsa Cikin Sakon Ta’azziyar Daya wallafa, Dauke Dasa Hannun Mai Taimakamasa na musamman Kan Harkokin yada labarai Shazali farawa.

Kazalika shugaban karamar hukumar Kumbotso Amadadin ma’aikatan karamar hukumar ya Mika sakon ta’aziyya ga Darakatar Mulki ta karamar Hukumar Kumbotso Hajiya Umma Abbas Sunusi Wakiliyar Galadiman Kano da fatan Allah Swt ya kyautata makwanci.

A karshe yayi fatan Allah ya baiwa iyalai da Al’ummar jihar Kano Dama kasa Baki Daya Hakurin jure wannan Babban Rashi.

93 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Babbar Sallah: Gwamnatin Kano ta sanar da ranar rufe makarantu a jihar

Daga Rahama Umar Kwaru   Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da...

Ban San Taulaci ba Sai da na Zama Sarkin Kano – Sarki Sanusi II

Daga Isa Ahmad Getso Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi...

Iftila:I: Gwamnatin Kano ta Aiyana Ranar Litinin a Matsayin Ranar Hutu

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin...

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...