Atiku Abubakar da jiga-jigan PDP sun Isa Kotun Sauraren Kararrakin Zaɓen Shugaban kasa

Date:

Daga Safiyanu Dantala Jobawa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya isa gaban kotun yayin da ake sa ran kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa za ta saurari bukatarsa ​​ta neman a rika yada zaman kotun kai tsaye.

 

A ranar 8 ga watan Mayu ne Atiku ya gabatar da bukatar neman a ba da damar yada zaman kotun kai tsaye kan shari’ar da suka kaizababben shugaban kasa, Bola Tinubu, wanda aka fara ranar Litinin.

Yayin da ya isa kotun daukaka kara ta Abuja, wurin zaman kotun a ranar Alhamis, tsohon mataimakin shugaban kasar yana tare da tsohon gwamnan jihar Cross River, Liyel Imoke da tsohon gwamnan jihar Adamawa, Bonny Haruna, sai tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, da dai sauran manyan jam’iyyar su ta PDP.

Yadda wata bazawara ta yi Garkuwa da yarta don neman kuɗin shiga Fina-finan Hausa a kano

Har ila yau a cikin yan rakiyar Atikun akwai dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar Kogi, Sanata Dino Melaye.

Gidan Talabijin na Channels ta ruwaito cewa Kotun za ta kuma saurari karar da jam’iyyar APM ta shigar na kalubalantar zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu ta yanke wa wani hukuncin daurin gidan yari bisa laifin kona tayoyin mota a Kano

Ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta jihar Kano ta...

Bayan ficewa daga PDP Dino Melaye ya koma ADC

Tsohon ɗan jamalisar dattawan Najeriya mai wakiltar Kogi ta...

Ƴan Ghana na zanga-zangar neman korar ƴan Nijeriya daga ƙasar

  Zanga-zanga ta ɓarke a Ghana inda ake zargin ƴan...

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...