Kotu ta yanke wa wani hukuncin daurin gidan yari bisa laifin kona tayoyin mota a Kano

Date:

Ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta jihar Kano ta bakin lauyanta Barista Bahijjah H. Aliyu, ta yi nasarar gurfanar da wani Ibrahim Abubakar a gaban kotu tare da samun shi da laifi har Kotun ta yanke masa hukunci saboda samunsa da laifin karya dokar hana gurbata muhalli da kuma dokokin kiyaye lafiyar al’umma.

Jami’an ‘yan sandan da ke sintiri a unguwar Tukuntawa Gidan Radio ne su ka kama Abubakar da lafin kona tayoyin mota, lamarin da ke da illa ga lafiyar jama’a sakamakon shakar hayaki mai guba.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan al’umma na ma’aikatar muhalli Murtala Shehu Umar ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

FB IMG 1753738820016
Talla

Biyo bayan korafin da mazauna yankin suka shigar, Daraktan kula da gurbatar muhalli Ibrahim Nasir ya jagoranci tawagarsa zuwa yankin domin duba lamarin, lamarin da ya kai ga shigar da kara a kotun majistare. A yayin shari’ar, masu gabatar da kara sun gabatar da kwararan hujjoji da ke nuna mummunar illar da abin da wanda ake tuhuma ya yi.

Bayan ficewa daga PDP Dino Melaye ya koma ADC

A hukuncin da Mai shari’a Auwalu Yusuf ya yanke, an yanke wa Abubakar hukuncin daurin watanni uku a gidan yari ko biyan tara. Alkalin kotun ya gargadi wanda ake kara da ya guji sake aikata laifin.

Ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta yaba da hukuncin kotun, inda ta jaddada kudirinta na kare muhalli da lafiyar al’umma a jihar Kano. Muna kira ga duk mazauna wurin da su bi ka’idodin muhalli kuma su guji ayyukan da ke cutar da muhalli da lafiyar jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...

Rundunar Sojin Amuruka ta kammala tsara yadda za ta kawo wa Nigeria hari

  Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar...

Kalaman Trump: Gwamnatin Nigeria ta Fara tattaunawa da Gwamnatin Amuruka

Gwamnatin Najeriya ta ce a gwamnantance tana tattaunawa da...

Ba zan bar Siyasa ba har lokacin da zan bar Duniya – Mal Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce...