Daga Sani Idris Maiwaya
Shugaban kwamitin karbar mulki na NNPP ƙarƙashin jagorancin Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya zargi gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje da sayar da hukumar kula da tsarin ayyukan kwangila wato Kano State Procurement Bureau wadda aka fi sani da Due Process ga ɗan gwamna Abba Ganduje.
“Muna da labarin an sayarwa da dan gidan gwamnan kaddarorin gwamnati sama da guda dari, sannan ba shi kadai ba mu duk wanda ya sayi kayan gwamnati, insha Allah zamu baiwa zaɓaɓɓen gwamnan Abba Gida-gida shawarar ya kwace duk irin wadancan kaddarorin”. Inji Baffa Bichi
Baffa Bichi ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci hukumar kula da tsarin ayyukan kwangila dake kan titin zuwa gidan gwamnatin kano.
Mutane 7 Sun Rasa Rayukansu Bayan Sun Sha Wani Shayi A Gidan Biki A Kano
Baffa Bichi yace abun takaici ne yadda gwamna Ganduje da mukarrabansa ke ci gaba da wadaka da kadarorin gwamnati, abun da suka ce ba zasu lamunci hakan ba.
Yadda wata bazawara ta yi Garkuwa da yarta don neman kuɗin shiga Fina-finan Hausa a kano
” Ba wai kwace kaddarorin kawai zamu bada shawarar ayi ba, sai mun bada shawarar an gurfanar da wadanda aka baiwa da wadanda suka sayi kaddarorin don magance irin wanana rashin kishin, ace ka sayarwa da danka wajen da akai masa kimar kudi samar da Miliyan 100 akan kudi kasa da Miliyan 10″.
Bichi yace idan gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf ta zo, dole ne su dubi irin wadannan kadarorin don dawowa da al’ummar jihar kano su.