Daga Rahama Umar Kwaru
Kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yi watsi da karar da jam’iyyar Action Peoples Party (APP) ta shigar na kalubalantar zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
A ranar Laraba ne kwamitin shari’a mai mutane biyar karkashin jagorancin Mai shari’a Haruna Tsammani ya yi watsi da batun bayan da jam’iyyar ta sanar da janye karar ta.
A zaman da aka ci gaba da sauraron karar, lauyan APP, Obed Agu Esq ya bayyana cewa jam’iyyar da dan takararta na shugaban kasa, Simon Nnadi, sun yanke shawarar janye karar.
Sai dai bai bada wani cikakken dalili ba.
A zaman farko da kotun ta yi a ranar Litinin, a yayin zama share faggen sauraron karar Agu ya bukaci kotun da ta tilasta wa Tinubu da APC su aminca cewa ba su suka yi nasara a zaɓen ba, saboda yadda APC suka tafka magudi a zaben .
Sai dai lauyoyin APC da Tinubu, Lateef Fagbemi da Wole Olanipekun, manyan Lauyoyin Najeriya, sun sanar da kotun da za ta yi maganin matsalolin a lokacin da ya dace.
Jam’iyyar a cikin karar ta bukaci kotun da ta soke takarar, Bola Tinubu bisa zargin rashin cancantar sa na tsayawa takara Shugaban kasa.
Sun kuma bayyana cewa INEC ta gaza yin aiki da dokar zabe ta 2022 ta tanada, ta hanyar hana fitar da sakamakon zabe, wanda hakan ya sa su yi nasara a zaben, inda suka kara da cewa an sami cin hanci da rashawa a zaben .
Sun kuma kara da cewa APC da Tinubu ba su samu rinjayen kuri’un da aka kada a zaben ba, wanda ya hada da tilascin samun kashi 25 na kuri’un da aka kada a babban birnin tarayya Abuja.