Hukumar Da’ar Ma’aikata ta bukaci Tinubu ya bayyana kadarorinsa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Hukumar dake kula da Da’ar Ma’aikata ta kasa ta ce dole ne zaɓaɓɓen shugaban Nigeria Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da gwamnonin ƙasar 28 da ke jiran rantsuwa su bayyana kadarorinsu kafin ranar 29 ga watan Mayu.

 

Mai magana da yawun hukumar Mrs Veronica Kato, ne ya bayyana hakan kamar yadda majiyar kadaura24 jaridar the Punch ta rawaito a yau Litinin.

Ya cebayyana kadarorin, wani ɓangare ne na shirye-shiryen shan ratsuwar kama aiki ga zaɓaɓɓun shugabannin kamar yadda dokar ƙasar ta tanadar.

Bankwana: Ganduje ya yafewa malaman makaranta kudaden gidaje

Haka kuma hukumar ta ce su ma zaɓaɓɓun ‘yan majalisun wakilai da na dattawa za su bayyana nasu kadarorin kafin ranar 5 ga watan Yuni lokacin da za a rantsar da su.

Mrs Kato, ta ce da yawa daga cikin zaɓaɓɓun sun fara karɓar fom ɗin bayyana kadarorin a rassan ofisoshin hukumar da ke faɗin jihohin ƙasar, kuma ana sa ran za su mayar da fom ɗin zuwa ofisoshin tare da bayyana kadarorin kafin ranar rantsar da su.

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa masu riƙe da muƙaman siyasa su bayyana kadarorin da suka mallaka a lokacin da za su kama aiki da kuma a lokacin da suka kammala wa’adin mulkinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...