Na so ‘ya’yana su zama ‘yan jarumai a Kannywood amma suka ki – Ali Nuhu

Date:

Daga Halima Musa Sabaru

 

Shahararren jarumin fina-finan Najeriya Ali Nuhu ya bayyana cewa ya so ‘ya’yansa su zama jaruman fina-fina amma kowanne su yaki ya zabi abun da suke so su zama a rayuwar su.

 

Nuhu ya ce dansa, Ahmad mai shekaru 16 ya fi sha’awar wasan kwallon kafa yayin da diyarsa Fatima ke da sha’awar karatun alakar kasa da kasa a jami’a.

A wata hira da ta yi da BBC Hausa, tauraron fina-finan ya musanta rade-radin da ake yi cewa jaruman Kannywood ba sa son sa ‘ya’yan su a sana’ar.

Ya ce “Gaskiya na fi son dana ya zama jarumi amma ya dage cewa yana da sha’awar kwallon kafa don haka na tallafa masa domin a zamanin nan bai kamata ka tilasta wa yaranka ya bi rabinka a abun da ya shafi rayuwar sa ba.

Hafsat Shehu ta bayyana Mawuyacin Halin da ta Shiga Bayan Rasuwar Ahmad S Nuhu

“A matsayinka na uba idan ka gano abun da danka yake sha’awa a game da sana’a, dole ne ka tallafa masa don ya cimma burinsa. A gare ni, na fi son in yi aiki da shi amma ya dage kan baya so shi yafi son kwallon kafa shi yasa nake bashi gudunmawar da yake bukata.

Kannywood: Tarihin Rayuwar Jaruma Rahama Sadau

“Fatima ta yanke shawarar kin yin wasan kwaikwayo tun tana shekara 13, ta so ta karanci dangantakar kasa da kasa, yanzu haka tana gab da kammala matakin aji na 3 a jami’a kuma godiya ta tabbata ga Allah tare da kwarin gwiwarmu, tana cikin daliban da ke samun maki Mai yawa a ajin su.”

 

Dangane da yadda masana’antar fina-finan Hausa ta ke, Ali Nuhu ya ce an samu ci gaba, inda ya kara da cewa sana’ar na ci gaba da habaka sosai, musamman ganin yadda kamfanonin Netflix da Amazon suka shiga harkar ka’in da na’in .

 

“Sana’ar tana ci gaba cikin sauri, musamman ganin yadda Netflix da Amazon suka bullo a Najeriya kuma a can yanzu sun fi mayar da hankali kan fina-finan Hausa, ka ga da a baya mun karaya mun daina shirya fina-finai, da ba mu cimma wannan gagarumar nasara ba. ”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...