Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
An haifi Rahama Ibrahim Sadau a ranar 7 ga Disamba, 1993. Jaruma ce kuma mai shirya fina-finai.
An haifi Sadau kuma ta girma a garin Kaduna, ta yi wasan raye-raye tun tana karama da kuma lokacin da take makaranta. Ta yi suna ne a karshen shekarar 2013 bayan ta shiga masana’antar Kannywood da fim dinta na farko Gani ga Wane.
Rahama Sadau tana fitowa a fina-finan Najeriya da dama a cikin harshen Hausa da turanci kuma tana daya daga cikin ‘yan wasan Najeriya da ke jin yaren Hindu na kasar india. Ita ce ta lashe kyautar jarumar (Kannywood) a gasar City People Entertainment Awards a 2014 da 2015.
Ta kuma lashe kyautar jarumar fina-finan Afirka a karo na 19 a shekarar 2015 ta African Voice.
Bankwana: Ganduje ya yafewa malaman makaranta kudaden gidaje
A shekarar 2017 ta zama shahararriyar jarumar Hausa ta farko da ta fito a cikin jerin jaruman mata goma da suka fi fice a Najeriya. A tsawon rayuwarta, Sadau ta kasance ‘yar wasan kwaikwayo ce mai yawan aiki, tana fitowa a fina-finai da kuma bidiyon wakoki.
An haifi Sadau a jihar Kaduna, dake arewa maso yammacin Najeriya wadda ita ce tsohuwar hedikwatar tsohon yankin Arewacin Najeriya, ta taso tare da iyayenta a Kaduna tare da yan uwanta guda hudu Zainab, Fatima Sadau, Aisha Sadau da Haruna Sadau.
Da dumi-dumi : Za mu iya hukunta Tinubu Kan kalamansa ga Shugaba Buhari – Abdullahi Adamu
A shekarar 2016 an san ta a matsayin “Face of Kannywood. A watan Oktoba na shekarar, Sadau ta fito a cikin jerin fina-finai a gidan talabijin na EbonyLife.
A shekarar 2017 ta kafa wani kamfani mai suna Sadau Pictures inda ta fitar da fim dinta na farko mai suna Rariya wanda suka hada da Ali Nuhu, Sani Musa Danja, Sadiq Sani Sadiq da Fati Washa.
A cikin 2022 Rahama Sadau ta fito tare da Vidyut jammwal a cikin fim din kasar india Mai suna Khuda Haafiz: Babi na 2 – Agni Pariksha bata taka rawa Mai yawa ba a cikin fim ɗin. Sadau ta shiga harkar fina-finan Kannywood ne a shekarar 2013 ta hannun Ali Nuhu.
Rahama sadau ta taka rawa a wasu fina-finan Amma bata shahara ba sai da yi wani fim mai Jinin Jikina wanda suka taka rawa tare da jarumi Ali Nuhu.
A ranar 3 ga Oktoba, 2016, kungiyar Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN), wacce ita ce babbar kungiya a Kannywood, ta dakatar da Sadau daga kannywood saboda fitowa a wani faifan bidiyo na soyayya tare da mawakin garin Jos, Classiq Q. Shekara daya bayan 2017, da ta rubutawa MOPPAN takardar ban hakuri.
A watan Janairun 2018 ne dai aka dage dakatarwar da aka sanya mata biyo bayan sa bakin gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Sadau ta mallaki Sadau Beauty, wurin gyaran jikin mata sannan kuma tana da shagon ice cream a jihar Kaduna mai suna Yogohamy. Kuma sadau na daga cikin jakadun kamfanin Maltina .
Jarumar ta kaddamar da gidauniyar agaji mai suna Ray of Hope. Kungiyar daliban Arewacin Najeriya ta nada ta a matsayin “Jakadiyar Zaman Lafiya”.
Rahama Sadau ta lashe kyautar gwarzuwar jarumar (Kannywood) a gasar City People Entertainment Awards a shekarar 2014. Ta sake maimaita hakan a shekara ta gaba. An zabe ta a matsayin mafi kyawun ‘yar wasan Afirka a bikin bayar da kyautar fina-finan Afirka karo na 19 a shekarar 2015 ta African Voice. Ta zama shahararriyar jarumar Hausa ta farko da ta fito a cikin Fitattun jaruman mata a Najeriya guda 10. A shekarar 2017, ta lashe kyautar Gwarzon Jarumar Afrika, wato voice of Afirka.
Daily news24