Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai ta Kasa Kuma Dan Majalisa Mai Wakiltar Kananan Hukumomin Tudun Wada da Doguwa Hon. Alhassan Ado Doguwa ya aike da sakon ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyar Masu Martaba Sarakunan Kano da Bichi ga iyalanta da al’ummar jihar Kano baki Daya.
Cikin Wata sanarwa Mai dauke da sa hannun Mataimaki na musamman ga Shugaban Majalisar Wakilai Auwal Ali Sufi utai ya aikowa Kadaura24 ya bayyana Rasuwar Hajiya Maryam Ado Bayero a Matsayin babban Rashi ba ga ga iyalanta kadai ba har da al’ummar jihar Kano Dana Kasa baki daya.
Alhassan Ado Doguwa yace Marigayiyar Mace ce Mai kyakykyawan Halaye Kuma uwa ce abar koyi saboda irin Tarbiyyar data baiwa ‘ya’yanta lokacin tana Raye.
“Salon yadda Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Dan uwansa Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero suke mulkar al’ummarsu ya nuna Hajiya Maryam Ado Bayero (Mai Babban Daki ) ta basu Tarbiyya ta Gari”. Inji Alhassan Ado Doguwa
Shugaban Masu Rinjayen yayi Mata addu’ar samun Rahamar Allah madaukakin Sarki tare d fatan Allah ya baiwa Iyalan da al’ummar jihar nan hakurin jire Wannan babban Rashin.