Daga Isa Ahmad Getso
Toshon shugaban Amurka Donald Trump ya ce magauta sun saka shi a gaba, a daidai lokacin da ya buɗe gangamin yaƙin sake dawowa muƙamin shugaban Amurrka
A gangamin da ya yi a jihar Texes Mista Trump ya yin iƙirarin cewa binciken ƙwaƙwaf da ake yi masa, ba wani abu ba ne face bi-ta-da-ƙullin siyasa.
Ɓacin ransa ya fi karkata kan tsohon lauyansa Michael Cohen .
Mista Trump da ya shafe tsawon makon da ya gabata yana ta magana kan binciken da ake yi masa a New York, na badaƙalar bai wa mai fina-finan baɗalar nan Stormy Daniels maƙudan daloli, inda ya kafe cewa bai san da wannan maganar ba.
Ko da yake yawancin maganganun da yake yi ba sababbi ba ne ga magoya bayansa ba, amma ya ce zai yi iya bakin ƙoƙarinsa don kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Ukraine cikin sa’a 24.