Barau Jibril ya lashe zaben Sanatan kano ta Arewa

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

 

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ayyana Sanata Barau I. Jibrin na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar Sanatan Kano ta Arewa .

 Farfesa Tijjani Magaji Bamanga wanda shi ne jami’in tattara sakamakon Zaɓen Sanatan Kano shi ne ya bayyana hakan  yau lahadi.
 Dan takarar na APC ya samu kuri’u 234, 652 wanda hakan ya sa ya samu nasara a kan babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar NNPP, Dr. Baffa Bichi wanda ya samu kuri’u 177, 014.
 Kafin bayyana sakamakon Zaɓen, sai da wakilin jam’iyyar NNPP ya bukaci jami’in zaben da ya bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba saboda zargin da yayi na cewa wadanda suka kada kuri’a sun fi wadanda aka tantance yawa.
 Sai dai jami’in zaben ya bayyana masa cewa babu isassun shaidun da zai ai hakan, inda ya bukace shi ya kai rahoton duk wani korafi ga INEC ko  kotu.
 Ga Sakamakon zaben a ƙasa:
 APC – 234, 652
 PDP – 12, 751
 NNPP – 177, 014
 LP – 1, 258

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta inganta walwala ma’aikatan dake kula da harkokin kudi – Babbar Akanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Gwamnatin jihar Kano ta ce za...

Fadar Shugaban Kasa ta magantu kan allunan tallan Tinubu da suka mamaye Abuja da Kano

Fadar shugaban Najeriya ta nesanta kanta daga wasu allunan...

Yansanda sun kama mafarauta huɗu ƴan asalin Jihar Kano a Edo

Rundunar yansanda ta kasa reshen jihar Edo ta tabbatar...

Kotu a Amurka ta umurci FBI da hukumomin yaƙi da ƙwayoyi su saki bayanan bincike kan Tinubu

  Kotun Ƙoli ta Ƙasa ta Washington D.C. a Amurka...