Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kammala rabon wasu daga cikin kayayyakin aikin zabe ga kananan hukumomi arba’in da hudu a jihar Kano kwanaki 4 kafin babban zaben 2023.
Jami’in zaben karamar hukumar Gwarzo Mal. Bello Ismail ya bayyana haka yayin taron masu ruwa da tsaki a ofishin sa dake karamar hukumar Gwarzo ta jihar kano.
Malam Bello Ismail ya kara da cewa ofishin zabe na karamar hukumar Gwarzo ya samu sama da kashi casa’in cikin dari na kayan da ba su da muhimmanci a halin yanzu.
A sanarwar da jami’in yada labarai na karamar hukumar Gwarzo Rabi’u Khalil ya aikowa kadaura24 yace Malam Isma’il ya kuma kara da cewa an sami wadanda suka chanza wuraren kada kuri’arsa zuwa sabbin rumfunan zabe a da aka samar a Damunawa, karkari, sabon garin Kayyu,unguwar Fulani da wasu garuruwa guda bakwai.
Da yake jawabi a lokacin taron mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa Gwarzo Alh.Sani Lakwaya ya tabbatar da cewa sun gargadi ‘ya’yan jam’iyyar su kan rashin da’a da tashin hankali a lokacin zabe a karamar hukumar Gwarzo.
A nasa jawabi mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP da shugaban jam’iyyar APM na karamar hukumar Gwarzo sun yi kira ga mambobinsu da su gudanar da gudanar da zaben cikin lumana tare da kaucewa daukar makamai a yayin gudanar da zaben 2023 mai zuwa.
A nasu bangaren jami’in hukumar Civil Defence Muhammad Hassan Usman da wakilin ‘yan sanda reshen Gwarzo Surajo Lawan sun tabbatar da cewa jami’an tsaro a shirye suke domin shawo kan duk wata barazana da ka iya tasowa a lokacin zabe da bayan zabe a karamar hukumar Gwarzo.
Sai dai sun gargadi mutane da su bi doka da oda a lokacin zabe mai zuwa.