Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Dan takarar majalisar wakilai na kura madobi da garun Mallam a tutar jam’iyyar APC Hon Dr Musa Iliyasu Kwankwaso ya fitar da wasu manufofin guda shida da yake son cimma idan al’ummar kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam.
Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana manufofin nasa ne yayin wata ganawa da yayi da Jaridar kadaura24.
Yace ya kamata duk wanda ya shirya Shugabanta ko wakiltar al’umma ya Samar da abubun da zai sanya a gaba idan Allah yasa ya zama abun da yake so ya zama, domin da haka ne zai iya magance matsalolin al’umma sa .
” Ni da yake nasan suwa zan wakilta hakan tasa na zauna na tsara abubuwan da zan Sanya a gaba idan na je majalisar wakilai ta kasa, ta yadda zan sami saukin sauke nauyin da al’ummar kananan hukumomin kura madobi da garun Mallam zasu dora min da yardar Allah”. Inji Musa Iliyasu
Yace zai Rika bin manufofin daya bayan daya har ya cimmu musu don inganta Rayuwar al’ummar kura madobi da garun Mallam cikin shekarun 4 farko da zai wakilci al’ummar sa a zauren majalisar wakilai ta kasa dake Abuja.
Ga manufofin da Hon. Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso ya ke son cimma idan ya zama dan majalisar tarayya.
1. Bunkasa aiyukan Noma
2. Bunkasa Ilimi a kananan hukumomin kura madobi da garun
3. Inganta harkokin kula da lafiyar al’umma.
4. Raya karkara
5 . Baiwa mata da matasa tallafin sana’o’in dogaro da kai
6. Wakilci na gari
Idan kuka cigaba da bibiyar mu zamu kawo muku bayani dalla-dalla akan wadancan manufofi na Dr. Musa Iliyasu Kwankwaso.