Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin zai rushe duk bankin da suka ki karbar tsofaffin kuɗi don mayar da shi makaranta domin inganta Ilimi a jihar kano.
Kadaura24 ta rawaito Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci wuraren da aka ajiye kayan abinchin da gwamnatin kano ta sayo domin rabawa ga al’ummar don sauka musu mawuyacin halin da ake ciki.

Gwamna Ganduje ya ce gwamnatin jihar kano bazata lamunci matakin da bankuna suka dauka ba na kin karɓar tsofaffin kudi, wanda hakan ya jefa al’ummar jihar kano cikin mawuyacin hali.

” Zamu kwace lasisin bankin da yaki karbar tsofaffin kuɗin sannan mu rushe bankin kuma mu mayar da shi makaranta don amfanin al’umma, kuma duk masu kasuwancin da suka ki karbar tsofaffin kuɗin to zamu rufe wurin”. Inji Ganduje
Yace saboda wahalar da ake cikin muka sayo kayan abinchin na miliyoyin nairori wadanda suka haɗar da shinkafa taliya da man girki don saukakawa al’umma wahalar da babban bankin Nigeria ya haifar.
Ganduje ya kara da cewa tuni aka samar da kwamitin da zai raba kayan lungu da sako na jihar kano don saukakawa al’umma .
A nasa jawabin shugaban kwamitin wanda shi ne dan takarar mataimakin gwamnan kano a jam’iyyar APC Hon Murtala Sule Garo ya ce an siyo shinkafa buhu sama da buhu Dubu 90 sai masara Dubu 22 sai taliya buhu Dubu 48 da kuma man jirki dubu 25.
Ya bada tabbacin zasu yi duk mai yiyuwa wajen ganin an raba kayan ga masu bukata da suke dukkanin kananan hukumomin jihar Kano don rage musu wahalhalun da tsarin babban bankin Nigeria ya fito da shi.