Shirin bunkasa noma da kiwo zai dauki nauyin karatun Dalibai 115 a kano

Date:

Daga Halima M Abubakar

Jami’in kula da Shirin bunkasa Noma da kiwo na jihar, Malam Ibrahim Garba Muhammad ya bayyana cewa, shirin zai dauki nauyin karatun matasa 115 yan jihar Kano don yin karatu a fannonin aikin gona.


 Babban Jami’in Shirin ya bayyana hakan ne yayin da yake zagayen nunawa Yan Kwamitin gudanawar Shirin irin aiyukan tallafi da Shirin ya gudana, yana mai bayanin cewa manufar ita ce a samar wa matasa kwarewa da ilimin da suka dace don kawo canji a fannin.


 “Za mu tallafa wajen horar da daliban 50 da suke da Diploma da Kuma Wasu 50 masu babbar diploma wato HND a jihar kano a kan al’amuran Kiwo, Gudanar da Shuka da Fadada Kimiyyar aiyukan gona a Kwalejojin Aikin Gona”, in ji shi, 

Tallan Shirin Boyayyen Masoyi


Cikin Wata sanarwa da Jami’in yada labaran Shirin Ameen K Yassar ya aikowa Kadaura24 yace Ibrahim Garba ya kara da cewa dalibai 10 da suka kammala karatun digiri na Farko da Kuma Mutane 5 Waɗanda Suka kammala Digiri na biyu dana uku da ke da kwarewa kan sarrafa Madara, za’a tallafa musu su don ci gaba da karatun su a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya da Jami’ar Bayero, Kano.


 “Wannan horo ne na gajeren lokaci da za mu ba da dama ga Kungiyoyin Manoma dana Makiyaya dama Masu Kasuwanci  amfanin Gona da dai sauransu, kokarin mu shi ne mu Inganta harkokin Noma da kiwo.” Inji Ibrahim Garba


 “Manufarmu ita ce mai da hankali ne kan inganta aikin gona da kiwo saboda muna da burin tallafawa gwamnati wajen sauya harkar noma daga ta al’adar zuwa ta Zamani don bunkasa tattalin arziki jihar Kano”.


 Shugaban kwamitin gudanarwa na KSADP kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna, wanda Babban Sakatare a Ma’aikatar Aikin Gona, Alhaji Balarabe Hassan Karaye ya wakilta, ya ce ana gudanar da Aiki  ne ba don kawai a tabbatar da cewa an aiwatar da ayyukan aikin ba  Kan kasafin da aka warewa Shirin ba har ma don ya dace tsarin da Duniya zata aminta da shi.

Tallan Shirin Bakin Gari


 “Kamar yadda kuka gani, muna shiga cikin hangen nesa na Gwamnatin Tarayya game da Noma kuma wannan aikin babban ci gaba ne na tabbatar da wadatar abinci da samar da aikin yi ga yawan jama’armu”.


 Ayyukan da Kwamitin Gudanarwar ya duba sun hada da ci gaba da fadada ofishin KSADP, da yin allurar rigakafin kananan dabbobi a karamar hukumar Bichi, gabatar da kayayyakin aiki ga manoma a karkashin shirin KSADP / SAA na sanya baki da kuma gyaran madatsar ruwa ta watari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...