Hukumar Hisbah ta Haramta Amfani da mutum-mutumi wajen ga teloli da masu sayar da kaya

Date:

Hukumar Hizbah ta Jihar Kano ta haramta wa teloli da masu shaguna amfani da mutum-mitumi wajen tallafa samfuran ɗinkunan su, ko kayan sayarwar su.

Premium times ta rawaito kwamandan Rundunar Sheikh Haruna Ibn Sina ne ya bayyana haka, inda ya ce kafa mutum-mitimin mai kama da gunki, ya saɓa wa Musulunci.

A Kano dai yawancin teloli da masu kantinan sayar da kayan zamani su na amfani da mutum-mutumin roba, wanda ake sa wa kaya, domin kwastomomi su ka yadda samfurin suturar ke bin dirin-jiki.

Sai dai kuma daga ranar Laraba Hisbah ta yi hani ga yin amfani da su, kuma hukumar ta ce za ta fara bi shagunan teloli da kantinan sayar da kayayyakin zamani ta na kama duk wanda ya karya wannan doka.

Hukumar Hizbah dai tun farkon kafa ta ne ta haramta sha, sayarwa da safarar giya a fadin jihar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abun da ya faru a Rano ba sai sake faruwa – Shugaban karamar hukumar ya tabbatar

Daga Abdulmajid Habib Tukuntawa   Shugaban karamar hukumar Rano malam muhd...

Bayan ganin wata Zulhijja, Saudiyya ta sanar da Ranar Arfat

Hukumomi a kasar saudiyya sun tabbatar da ganin jinjirin...

Kotu ta yanke hukuncin kisa ga matashin da ya kona masallata a Kano

Babbar Kotun Shari’a da ke Kano ta yanke hukuncin...

Sarkin Musulmi ya umarci yan Nigeria su fara duban watan Zulhijja

Fadar mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar...