Daga Rahama Umar Kwaru
Anyi kira ga Gwamnatin Najeriya ta binciki zargin kisan gilla da wasu mutane dake sanye da kayan Sojoji a Kasar Burkinafaso suka yiwa wasu yan Najeriya 17 da suke kan hanyarsu ta zuwa Kasar Senigal domin halartar Mauludin Shehu Ibrahim Inyass.
Kadaura24 ta rawaito annan kira na kunshe ne cikin wata sanarwar Ta’aziyya da Kungiyar Samarin Tijjaniyya ta Kasa ta fitar mai dauke dasa hannun shugaban Kungiyar Barista Habibu Dan Almajiri da Babban Sakataren Kungiyar Shehu Tasiu Ishaq.
Mutanen dai suna kan hanyarsu ne ta zuwa garin Kaulaha dake kasar Senigal a motoci wadanda suka tashi daga nan Najeriya domin halartar Mauludin Shehu Ibrahim Inyass, kamar yadda aka saba gabatarwa duk shekara a can garin Madinatu Kaulaha.
Yayin da ake zargin Sojojin Kasar Burkinafaso, sun bude musu wuta bayan sun tsayar da motocinsu kuma suka harbesu har lahira.


Daganan sanarwar tayi addu’ar Allah ya jikansu kuma ya karbi shahadarsu yakai rahama kabarinsu ya bawa iyalansu hakurin jure rashinsu.