Zan sake fasalin Nijeriya a wata shidan farko na mulki na

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zai tabbatar da sake fasalin Najeriya cikin watanni shida na mulkinsa idan an zabe shi.

 

Ya bayyana haka ne a babban taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP da aka gudanar a Abuja.

 

Abubakar, wanda ya samu wakilcin tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Okwesilieze Nwodo, ya ce an kammala isassun ayyukan bincike da ake bukata domin sake fasslin Najeriya.

Talla

Nwodo shi ne mataimakin darakta, bincike da dabaru, na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, PCC.

Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil

Ya ce Najeriya za ta samu daidaito ne idan kowane yanki ya mallaki albarkatun kasa.

 

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya tuna cewa ana kafa ci gaban zamantakewa da tattalin arziki lokacin da yankuna ke sarrafa albarkatun su.

“Lokacin da muke magana game da sake fasalin tsarin mulki, a cikin watanni shida na farko, da kasar nan ba za ta zama abin da kuke gani a yau ba.

“An yi aiki da wannan kuma ina jira kawai a rantsar da ni a ranar 29 ga Mayu kuma za a fitar da tsare-tsaren.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...