Allah ya yiwa Mahaifiyar Maryam Booth ta Rasuwa

Date:

Yar wasan fina-finan Kannywood, Hajiya Zainab Booth, wadda ke jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta rasu bayan fama da rashin lafiya.

Ta rasu ne a birnin Kano da daren Alhamis, a cewar danta Umar Booth, a tattaunawarsa da Manema labarai.

Ta rasu tana da shekaru 61 a duniya.

“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un, hakika Allah cikin ikonsa ya yi wa mahaifiyarmu Hajiya Zainab Booth rasuwa bayan fama da rashin lafiya, ta rasu a daren Alhamis da misalin karshe 9 na dare, za a yi jana’izarta a yau Juma’a idan Allah ya kai mu.

Ta rasu ta bar ‘ya’ya hudu, maza biyu da mata biyu, wato Ni Umar, sai Amude da Maryam da kuma Sadiya, sai jikoki guda biyu,” in ji Umar.

Maryam Booth da Mahaifiyarta Zainab Booth

Umar ya kara da cewa za a tuna da Hajiya Zainab Booth da son zumunci da yawan yin addu’a, sannan ita din uwa ce ga kowa don haka ne ma duk inda ta shiga za ka ji ana kiranta Mama, Mama.

A kwanakin baya ne dai marigayiyar ta yi fama da rashin lafiya lamarin da ya kai har an yi mata aiki a kwakwalwa, kamar yadda ‘yarta Maryam Booth ta dinga wallafa hotunan a shafukan sada zumunta.

Marigayiyar ta kasance daya daga cikin taurarin Kannywood da ‘ya’yanta uku suka kasance su ma taurari

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...