Kungiyar Daliban Arewa ta Karrama Wasila M Ibrahim

Date:

Daga Rabi’u Usman

Biyo Bayan Faduwar Jarrabawar Qualifying na Dalibai yan Aji 3 da Kuma Masu Share Faggen Shiga Jami’a a Nan Kano.

Masu Salon Magana Kance “ya ba Kyauta Tukuici”, a Hannu guda Kuma, Wasu Shugabannin Daliban Jami’a na Arewacin Kasar Nan ne Suka Karrama Hajiya Wasila Musa Ibrahim Shugabar Kamfanin Naja’atu Petroleum and Global Business Bisa Kokarin ta na ganin Ilimi ya Samu Cigaba a Jihar Kano Dama Kasa baki Daya.

Shugaban Kungiyar Daliban Jami’a na Arewacin Kasar Nan, ta Bakin Babban Maga Takardar Kungiyar Comrade Ja’afar S Musa, Sun yaba da Kokarin da Wasila keyi na ganin ta Taimakawa Marayu, Zawarawa, Matasa harma da Marasa Karfi ta Fannoni Daban Daban, inda yace Hajiya Wasila ta Zama “Mace Mai Kamar Maza Kwari ne Babu”, Akan Kokarin Tallafawa Mabukata Marayu da Marasa Karfi a Fadin Sassan Unguwannin Kwaryar Birnin Kano da Kewayen ta.

A Nata Bangaren Hajiya Wasila Musa Ibrahim ta Bayyana Jin Dadin ta Dangane da Wannan Lambar Yabo da Daliban Suka Bata, harma ta lashi Takobin Kara Zage Damtse Wajen Ganin ta Ninka Abin da take yi na Taimakawa Al’ummar Musulmi a Fadin Jihar Kano Dama Kasar Mu Nigeria Baki Daya.

Daga Nan tayi Kira ga Kafatanin Masu Rike da Mukamin Siyasa da Masu Hannu da Shuni dasu Kasance Masu Taimakawa Al’ummar Musulmi Musamman a Wannan Lokacin da ake Cikin Matsin Rayuwa.

Idan dai Ba’a Manta ba a Makonni Biyu da Suka Gabata Wasu Kungiyoyi Masu Zaman Kansu a Nan Kano harma da Kungiyar Dalibai na Jami’ar Yusuf Mai Tama Sule Sun Bata Lambar Yabo Bisa Kokarin Samar da Sana’oin Dogaro da Kai ga Matasa Maza da Mata a Fadin Jihar Kano baki daya.

148 COMMENTS

  1. Бой Усик Джошуа Anthony Joshua vs Oleksandr Usyk Дуелът Джошуа – Усик ще определи кой ще разполага с 3 от 4-те най-престижни колани (wba, wbo и ibf) и кой ще може да се нарича световен шампион. Разбира се, 31-годишният британски състезател е големият

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...