Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya amince a fitar da Naira miliyan 500 ga daukacin kananan hukumomin jihar 34 domin tara Jama’ar jihar sakamakon ziyarar aiki ta kwanaki biyu da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai jihar a watan Janairu. 26 da 27.
Jaridar Solace Base ta Sami tabbacin hakan ne cikin wata wasika dake dauke da amincewar gwamna Masari , inda ta bayar da izinin sakin “N14,695,588.00 ga dukkanin kananan hukumomin guda 34 da ya kai N499,650,000.00 (Miliyan dari hudu da casa’in da tara, Naira dubu dari shida da hamsin kacal). Kuma wadannan kudaden an fitar da su ne daga asusun hada ka na kananan hukumomi 34 da ke jihar don fito da al’ummar jihar domin su tarbi Shugaban kasa a ziyarar aiki da zai kai jihar Katsina daga ranar 26-27 ga Janairu, 2023.
Yahuza S. Ibrahim, ne yasa hannu a wasikar a madadin babban sakataren gidan gwamnatin jihar Katsina da kuma aka turawa kwamishinan kananan hukumomi da masarautu n jihar.

A cikin kwafin wasikar da kadaura24 ta gani an tura wasikar zuwa ofishin babban akanta janar na jihar, ma’aikatar kudi da kuma babban mai binciken kudi domin gaggauta biyan kudin kafin zuwan Muhammadu Buhari kafin ranar 26 ga watan Janairu.

Jihar Katsina dai kusan kashi 70 cikin 100 na mazauna jihar na fama da talauci, kamar yadda wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar a watan Satumban da ya gabata, wasu da dama na ganin magudan kudaden da aka fitar kawai don tarbar shugaban kasar almubazzaranci ne.