An yaye marayu 100 da dan majalisar Wudil da Garko ya ɗauki nauyin koya musu sana’o’i

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Marayun nan guda 100 da dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Wudil da Garko Engr. Muhammad Ali Wudil ya dauki nauyin koya musu sana’o’in dogaro da kai sun kammala daukar horon.
Da yake jawabi a wajen bikin yaye marayun dan majalisar yace ya ɗauki gabarar daukar nauyin koya musu sana’o’in ne don su dogaro da kawunansu kuma suma su sami damar da zasu tallafawa wasu.
” A wannan lokaci ba abun da zaka baiwa matashi musamman maraya da ya wuce Ilimi da kuma sana’a, saboda da su ne zai iya tsayawa ya San wanene shi Kuma har ya ji kan wasu shima kamar yadda akai masa, Amma idan ba a taimake su do rayuwar su da ta sauran al’umma tana cikin hadari”. Engrn Muhammad Ali
Talla
Ya kara da cewa tuni ya biya kudin da aka nema don koya musu sana’o’in Kuma a wajen bikin ya baiwa kowanne su Yan kuɗaden da zasu yi amfani da su wajen yin jari don fara sana’o’in da suka koya.
Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil
Dan majalisar na Wudil da Garko ya yi kira da Sauran yan siyasa da masu hannu da shuni da su himmatu wajen inganta Rayuwar matasa musamman marayu domin yin hakan zai rage yawaitar laifukan da ake yi a cikin al’umma.
Wasu daga cikin marayun da suka zanta da kadaura24 sun nuna farin cikinsu tare da bada tabbacin zasu yi amfani da sana’o’i da jarin da aka basu don inganta Rayuwar da ta sauran yan uwan su.
Sun Kuma bada tabbacin zasu saka alheri da alheri idan ranar zabe taron don sauran matasan yankin Wudil da Garko suma su dade suna amfanar irin wannan tagomashi da dan majalisar su na tarayya yayi musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...