Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi kakkausar suka kan hare-haren ’yan bindiga da aka ruwaito sun faru a wasu sassan kananan hukumomi hudu na jihar, tare da tabbatar wa al’ummomin da abin ya shafa cewa gwamnatinsa na daukar matakan da suka dace domin kara karfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa Kadaura24.

Wuraren da hare-haren suka shafa sun hada da Chiromawa da ke Karamar Hukumar Garun Mallam, Beli a Rogo, Bebeji, da kuma wasu al’ummomin da ke kusa da Gwarzo.
Gwamna Yusuf ya jajanta wa wadanda hare-haren suka rutsa da su da iyalansu, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin mai matukar tayar da hankali kuma wanda ba za a amince da shi ba.
Ya tabbatar wa al’ummomin da abin ya shafa cewa gwamnati za ta dauki dukkan matakan da suka dace, tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro, domin dakile sake aukuwar hare-hare da kuma dawo da kwarin gwiwar jama’a kan tsaro.
Gwamnan ya ce an umarci hukumomin da abin ya shafa da su kara kaimi wajen sa ido, tattara bayanan sirri da kuma inganta tsarin daukar matakin gaggawa a wuraren da lamarin ya shafa.
Ya kuma bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu tare da kauce wa duk wani mataki da zai iya kara dagula al’amura, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnati na aiki kafada da kafada da jami’an tsaro domin shawo kan matsalar.
Haka kuma, Gwamna Yusuf ya yi kira ga al’umma da su ba jami’an tsaro cikakken hadin kai tare da samar musu da sahihan bayanai da za su taimaka wajen dakile hare-haren da kuma cafke wadanda ke da hannu a aikata laifukan.
Gwamnan ya yabawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, tare da bukatarsu da su ci gaba da gudanar da ayyukan leken asiri da sahihan bayanai domin kare al’ummomin da ke cikin hadari a fadin jihar.

Ya kuma yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasa rayukansu, Ya ba wadanda suka samu raunuka lafiya cikin gaggawa, sannan Ya dawo da duk mutanen da aka yi garkuwa da su cikin aminci.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin daukacin al’ummar Jihar Kano, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a sassan jihar.