‎Kungiyoyin Makarantun Islamiyya Sun Nada Isah Ado Muhammad Badawa a Matsayin Majidadin Makarantun Islamiyya

Date:


‎Kungiyoyin makarantun Islamiyya na Ƙaramar Hukumar Nassarawa da ƙungiyar tallafa wa matasa ta Kudancin Nassarawa, da ke Unguwar Badawa, sun gudanar da taron Maulidi, inda suka nada Sakataren Jam’iyyar APC na Mazabar Giginyu, Hon. Isah Ado Muhammad Badawa, a matsayin Majidadin Tallafawa Makarantun Islamiyya.

‎Babban malamin Unguwar Badawa, Malam Gwani Kanzu Badawa, tare da takwaransa Malam Saminu Gidan Salati, sun bayyana cewa an bai wa Hon. Isah Ado Muhammad Badawa wannan sarauta ne bisa la’akari da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen tallafa wa harkokin addinin Musulunci, da kuma taimaka wa matasa da marayu a yankunan Ƙaramar Hukumar Nassarawa.

IMG 20260704 WA0007
Talla


‎Da yake jawabi, Injiniya Usman Taye Ahmed, Daraktan Sashen Ayyuka na Ƙaramar Hukumar Nassarawa, ya bayyana farin cikinsa kan karrama Hon. Isah Ado Muhammad Badawa da wannan sarauta, yana mai cewa an sanya wa kowa abin da ya dace da shi.

‎Shi ma a nasa jawabin, Sakataren Jam’iyyar APC na Mazabar Giginyu kuma sabon Majidadin Tallafawa Makarantun Islamiyya da Matasa, Hon. Isah Ado Muhammad Badawa, ya gode wa ƙungiyoyin da suka ga cancantarsa tare da ba shi wannan matsayi.

‎Isah Ado Muhammad Badawa ya ce bai san cewa al’ummar yankunan Ƙaramar Hukumar Nassarawa na lura da irin gudunmawar da yake bayarwa ba, har sai da suka yanke shawarar karrama shi da wannan sarauta.

IMG 20260704 WA0005
Talla


‎Ya kuma gode wa waɗanda suka karrama shi bisa la’akari da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen tallafa wa makarantun Islamiyya, matasa da kuma harkokin siyasa.

‎A ƙarshe, ya yi kira ga al’ummar yankunan da su ci gaba da ba Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, goyon baya, tare da ba shi damar sake jagorantar jihar a wa’adi na biyu.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano Ta Musanta Zargin Kungiyar Tracker na Ware Naira Miliyan 235m Don Gina Azuzuwa A Sumaila

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta wani rahoto da ƙungiyar...

‎Ɗan Ganduje ya fice daga Kwankwasiyya ya koma APC

‎ ‎Abdulaziz Umar Ganduje, babban ɗan tsohon Gwamnan Jihar Kano...

Siyasar Shekarau da Ganduje da Abba ta zo ƙarshe a Kano – Kwankwaso

Mataimakin ɗan takarar jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata...

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin Hajjin 2027, ta ƙara wa’adin biyan kuɗi

‎ ‎Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar...