Gwamnatin Kano Ta Musanta Zargin Kungiyar Tracker na Ware Naira Miliyan 235m Don Gina Azuzuwa A Sumaila

Date:

Gwamnatin Jihar Kano ta musanta wani rahoto da ƙungiyar Tracka ta fitar, wanda ya zargi gwamnatin da ware sama da Naira miliyan 235 a kasafin kuɗin shekarar 2025 domin gina azuzuwa a Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Massu, da ke Ƙaramar Hukumar Sumaila.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai, inda ya ce zargin ba shi da tushe.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Waiya ya ce babu wata shaida da ke nuna cewa an biya kuɗin da ake magana a kai, ko kuma an aiwatar da aikin, kamar yadda rahoton aiwatar da kasafin kuɗin jihar na zangon ƙarshe na shekarar 2025 ya nuna.

Ya bayyana cewa kasafin kuɗin Jihar Kano na shekarar 2025 ya kai Naira biliyan 719 da miliyan 557, inda aka ware Naira biliyan 168 da miliyan 350 ga ɓangaren ilimi.

A cewar kwamishinan, kuɗaɗen da aka ware wa ilimi sun haɗa da gyaran makarantu, ɗaukar malamai, samar da kayan koyarwa da na makaranta, tsaro, da kuma aiwatar da manyan ayyukan ilimi a ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Kwamishinan ya ƙara da cewa babu wani aiki mai suna GGSSS Massu, Sumaila, wanda aka ware masa sama da Naira miliyan 235 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2025, ko kuma a cikin takardun amincewar Majalisar Zartarwar Jihar Kano.

Ya ce dukkan ayyukan gwamnati ana tantance su tare da bin ƙa’idojin da suka dace kafin fara aiwatar da su.

Waiya ya bayyana cewa a halin yanzu Ma’aikatar Ilimi ta jihar da Hukumar SUBEB suna gudanar da bincike kan ayyukan ilimi a Ƙaramar Hukumar Sumaila, yana mai cewa za a bayyana sakamakon binciken ga jama’a da zarar an kammala shi.

IMG 20260704 WA0005
Talla

Kwamishinan ya kuma ƙalubalanci ƙungiyar Tracka da sauran ƙungiyoyin fararen hula da su gabatar da shafin kasafin kuɗin da suka dogara da shi, da lambar aikin, da kuma shaidar bayar da kwangilar.

Ya ce ya kamata ƙungiyoyin su kuma gabatar da shaidar biyan kuɗi, sunan ɗan kwangilar da bayanan ziyarar binciken da suka ce sun gudanar a Massu, domin tabbatar da sahihancin zargin da suka yi.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Kungiyoyin Makarantun Islamiyya Sun Nada Isah Ado Muhammad Badawa a Matsayin Majidadin Makarantun Islamiyya

‎ ‎Kungiyoyin makarantun Islamiyya na Ƙaramar Hukumar Nassarawa da ƙungiyar...

‎Ɗan Ganduje ya fice daga Kwankwasiyya ya koma APC

‎ ‎Abdulaziz Umar Ganduje, babban ɗan tsohon Gwamnan Jihar Kano...

Siyasar Shekarau da Ganduje da Abba ta zo ƙarshe a Kano – Kwankwaso

Mataimakin ɗan takarar jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata...

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin Hajjin 2027, ta ƙara wa’adin biyan kuɗi

‎ ‎Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar...