Gwamna AbdulRazaq na gina sabuwar makomar noma a jihar Kwara

Date:


‎Jihar Kwara na ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren bunƙasa harkar noma domin tabbatar da samar da isasshen abinci da kuma inganta rayuwar manoma.

‎A ƙarƙashin shirin sauya fasalin noma na tsawon shekaru 10 da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq samar, an fara sauya noma daga na dogaro da kai zuwa tsarin zamani da zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.

IMG 20260704 WA0007
Talla

‎Gwamnatin ta samar da sama da kilomita 210 na hanyoyin karkara domin haɗa al’ummomin manoma da kasuwanni, tare da inganta amfani da injinan noma, ban ruwa, dabarun noma masu jure sauyin yanayi, sarrafa amfanin gona da kiwon dabbobi.

‎Haka kuma, an tantance sama da manoma 100,000 ta hanyar bayanan halittu (biometric) tare da gano wuraren da gonakinsu suke, domin tabbatar da cewa tallafin gwamnati na isa ga manoman da suka cancanta.

‎Gwamnatin ta ce zuba jari a kayan aikin noma, kayayyakin amfanin gona, hanyoyin karkara, ban ruwa da kiwon dabbobi na taimakawa wajen ƙara yawan amfanin gona da samar da ayyukan yi da hanyoyin samun kuɗi masu ɗorewa.

IMG 20260704 WA0005
Talla

‎A cewar Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, harkar noma ba ta tsaya ne kawai wajen samar da abinci ba, illa tana kuma da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa manoma, bunƙasa al’umma da samar da kyakkyawar makoma ga al’ummar Kwara.

‎“Girbin nasara yana farawa ne da shugabanci mai hangen nesa.”

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyarar dubiya ne...

Amincin Tinubu Ga Barau Kan Harkar Tsaro Da Cigaban Kasa Daga Abba Anwar

Daga Abba AnwarA wani taron harkar tsaro da cigaban...

NAHCON ta Sanar da Kudin Aikin Hajjiin Badi

‎Hukumar Alhazai ta Najeriya, NAHCON, ta sanar da kuɗin...

Tinubu ya buƙaci INEC ta tabbatar da gaskiya da adalci a zaɓen Osun

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci Hukumar Zaɓe...