Tinubu ya buƙaci INEC ta tabbatar da gaskiya da adalci a zaɓen Osun

Date:

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro da aka tura jihar Osun su tabbatar da gudanar da zaɓen gwamnan jihar cikin lumana, gaskiya da adalci.

A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Juma’a, Tinubu ya ce INEC na da alhakin tabbatar da sahihancin tsarin zaɓen da kuma kare amincin sakamakonsa.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Shugaban ya buƙaci INEC ta yi amfani da zaɓen Osun a matsayin wata dama ta nuna shirinta na gudanar da babban zaɓen 2027 cikin inganci da gaskiya.

Haka kuma, ya umarci Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da aka tura jihar da su tabbatar da tsaron masu kaɗa ƙuri’a da jami’an zaɓe, tare da hana duk wani mai tayar da hankali kawo cikas ga zaɓen.

IMG 20260728 WA0005
Talla

Tinubu ya ƙarfafa wa al’ummar Osun gwiwa da su fito su kaɗa ƙuri’unsu cikin ’yanci, ba tare da tsoro ko barazana ba.

Ya jaddada cewa sakamakon zaɓen dole ne ya kasance abin da ya dace da muradin al’ummar jihar, yana mai cewa sahihancin zaɓen zai dogara ne kan yadda sakamakonsa zai bayyana zaɓin masu kaɗa ƙuri’a.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Alƙalin Alƙalan Kano ta duba shari’o’in fursunoni 82, ta bayar da umarnin sakin 7

‎ ‎Alkalin Alƙalan Jihar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki,...

‎Ranar Matasa: AHIP Ta Ce Bai Kamata Bambancin Yanayi Ya Hana Matasa Samun Damarmaki Ba

‎ ‎Yayin da duniya ke bikin Ranar Matasa ta Duniya...

Falakin Shinkafi ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar watan da aka haifi Annabi ﷺ

 Amb. Yunusa Yusuf Hamza, Falakin Shinkafi, ya taya al’ummar...

‎Waiya ya samu lambar yabo ta ƙasa kan ƙwarewa wajen yada bayanai a lokacin rikici

‎ ‎Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar...