‎Gwamna Abba Ya Lashe Kyautar WINSEC Bisa Nagartaccen Jagoranci, Waiya Ya Samu Lambar Yabo Kan Dabarun Sadarwa

Date:


‎Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya wakilci Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a taron Women in Security Summit (WINSEC) 2026, wanda Ƙungiyar Mata ‘Yan Jarida ta Ƙasa (NAWOJ) ta shirya a otal ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja.

‎A yayin taron, Kwamared Waiya ya karɓi Kyautar Girmamawa ta WINSEC a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Wanda kungiyar ta karrama shi bisa nagartaccen jagoranci wajen inganta zaman lafiya, tsaro da shugabanci nagari.

IMG 20260704 WA0007
Talla


‎Da yake jawabi bayan karɓar kyautar, Waiya ya bayyana cewa wannan karramawa wata shaida ce ta nagartaccen salon mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya mayar da hankali wajen kyautata rayuwar al’umma da samar da ingantattun ayyukan gwamnati.

‎Ya miƙa godiya ga masu shirya taron a madadin gwamnati da kuma al’ummar Kano, yana mai cewa wannan lambar yabo za ta ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da gudanar da mulki bisa gaskiya, riƙon amana da inganta ayyukan gwamnati.

‎Har ila yau, Waiya ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf murnar wannan gagarumar nasara, yana mai danganta lambar yabon da hangen nesansa da ingantaccen jagorancin gwamnan, wanda ya ce yana ƙarfafa gwiwar jami’an gwamnati su yi aiki tukuru domin ci gaban jihar.

‎Baya ga karɓar kyautar a madadin Gwamnan Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya shi ma ya samu Lambar Yabo Kan Ƙwarewa a Fannin dabarun Sadarwa (Strategic Communication) wanda ƙungiyar NAWOJ ta ba shi bisa irin gudunmawar da yake bayarwa wajen yaɗa bayanan gwamnati da kuma tafiyar da harkokin sadarwa cikin kwarewa.

IMG 20260728 WA0005
Talla


‎Waiya ya gode wa ƙungiyar bisa wannan karramawar har guda biyu da Wadda aka yi masa da kuma ta Gwamnan Kano, yana mai cewa lambobin yabon za su ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da inganta shugabanci da sadarwa domin amfanin al’umma.

‎A ƙarshe, Kwamishinan ya gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa wannan tagomashi da aka yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma shi kansa, yana mai cewa ya zamo wajibi a gare shi ya godewa Allah da wannan ni’imar.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

‎Tinubu ya bai wa EFCC umarnin buɗe asusun Gwamnatin Osun

‎ ‎ ‎Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Yaƙi da...

‎ EFCC ta bayyana dalilin dakatar da asusun gwamnatin Jihar Osun

‎ ‎Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya...

‎Da dumi-dumi: Matatar Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur da Dizal

‎ ‎Matatar Man Dangote ta sanar da rage farashin man...

Kwanaki 10 kafin zaɓen gwamna: EFCC ta rufe asusun gwamnatin jihar Osun

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta'annati...