Matatar Man Dangote ta sanar da rage farashin man fetur da take sayarwa ga dillalai daga Naira 1,215 zuwa Naira 1,165 kan kowace lita, wanda ke nuna an rage Naira 50.
Haka kuma, matatar ta rage farashin dizal daga Naira 1,650 zuwa Naira 1,570 kan kowace lita, inda aka samu ragin Naira 80.

matatar ta bayyana wannan sauyin farashi ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce matatar ta ɗauki wannan mataki ne domin ci gaba da tabbatar da samar da mai me inganci da farashi mai sauƙi ga kasuwar Najeriya.

A cewar sanarwar, sabon tsarin farashin ya tanadi cewa za a riƙa sayar da fetur ga dillalai kan Naira 1,165 kan kowace lita, maimakon Naira 1,215 da ake sayarwa a baya.
Hakazalika, an rage farashin dizal zuwa Naira 1,570 kan kowace lita, daga Naira 1,650, domin sauƙaƙa wa masu amfani da wannan nau’in mai da kuma tallafa wa harkokin kasuwanci da sufuri.