INEC za ta gudanar da zaɓen shugaban kasa na gwaji

Date:

Hukumar zaɓen Najeriya ta ce tana duba yiwuwar yin zaɓen shugaban ƙasar na gwaji, gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe a shekara mai zuwa.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ne ya bayyana haka a ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery, lokacin wata ziyara da ya kai shalkwatar hukumar zaɓen da ke Abuja, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

IMG 20260704 WA0007
Talla

Farfesa Amupitan ya ce hukumar na wannan shiri ne domin tabbatar da sahihanci da ingancin na’urorin zaɓen, la’akari da ƙorafe-ƙorafen da aka samu bayan zaɓukan 2023.

Ya ƙara da cewa INEC na duba yiwuwar gwada kayayyakin hukumar zaɓen gabanin babban zaɓen 2027 da ke tafe.

2027: INEC ta bayyana matsayarta ta kan rikicin jam’iyyar ADC

“Muna duba yiwuwar gwada duka kayyaki da na’urorin zaɓenmu, gabanin babban zaɓen da ke tafe, da kuma yiwuwar yin zaɓen shugaban ƙasa na gwaji, domin gwaja ingancin kayayyaki da na’urorin namu,” in ji shi Farfesa Amupitan.

IMG 20260704 WA0005
Talla

Ya ƙara da cewa matakin na daga cikin shirye-shiryen hukumar na inganta tsarin fasahar hukumar ciki har da tsarin tantance masu zaɓe da hanyar na’ura da amfani da shafin IRev wajen tura sakamakon zaɓe, da tsarin tsaron shafin.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dambarwa ta barke tsakanin Rundunar Hisbah da Hukumar tace fina-finai ta Kano

Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab'i ta Jihar Kano ta...

An naɗa DCF UM Sadiq a matsayin Sabon Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya a Kano

Babban Kwanturolan Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (Federal Fire...

Masu Buƙata ta Musamman a Nassarawa Sun Koka Kan Rashin Samun Tallafin Gwamnatin Kano

Shugabannin ƙungiyar masu buƙata ta musamman reshen ƙaramar hukumar...