Hukumar zaɓen Najeriya ta ce tana duba yiwuwar yin zaɓen shugaban ƙasar na gwaji, gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe a shekara mai zuwa.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ne ya bayyana haka a ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin jakadan Birtaniya a Najeriya, Dr Richard Montgomery, lokacin wata ziyara da ya kai shalkwatar hukumar zaɓen da ke Abuja, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

Farfesa Amupitan ya ce hukumar na wannan shiri ne domin tabbatar da sahihanci da ingancin na’urorin zaɓen, la’akari da ƙorafe-ƙorafen da aka samu bayan zaɓukan 2023.
Ya ƙara da cewa INEC na duba yiwuwar gwada kayayyakin hukumar zaɓen gabanin babban zaɓen 2027 da ke tafe.
2027: INEC ta bayyana matsayarta ta kan rikicin jam’iyyar ADC
“Muna duba yiwuwar gwada duka kayyaki da na’urorin zaɓenmu, gabanin babban zaɓen da ke tafe, da kuma yiwuwar yin zaɓen shugaban ƙasa na gwaji, domin gwaja ingancin kayayyaki da na’urorin namu,” in ji shi Farfesa Amupitan.

Ya ƙara da cewa matakin na daga cikin shirye-shiryen hukumar na inganta tsarin fasahar hukumar ciki har da tsarin tantance masu zaɓe da hanyar na’ura da amfani da shafin IRev wajen tura sakamakon zaɓe, da tsarin tsaron shafin.