Wani jami’in Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), Yusuf Isa Muhammad, ya ki karbar tayin cin hancin Naira 500,000 domin ya saki wata mota da take ɗauke da giya da ya kama a cikin birnin Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’in ya tare motar ne da daddare a kan titi Hadejia Road, inda bayan bincike aka gano takardar lodin kaya ta motar na nuna cewa motar ta dauko giya ne kuma ana kokarin kai giyar unguwar Sabon Gari.

Bayan kama motar, wasu mutane sun yi ƙoƙarin bai wa jami’in kuɗin cin hanci domin ya ƙyale motar ta wuce, amma ya ƙi amincewa da tayin, har ma ya ƙi bayar da lambar asusun bankinsa domin karɓar kuɗin.
Daga bisani, Yusuf Isa Muhammad ya kai motar tare da kayan da ke cikinta zuwa hedikwatar hukumar KAROTA, inda aka miƙa su ga Hukumar Hisbah ta Jihar Kano domin ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace a ƙarƙashin doka.

Da yake jawabi kan lamarin, Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Malam Aminu Daurawa, ya yaba da jajircewa da gaskiyar jami’in, yana mai cewa irin wannan hali abin koyi ne ga sauran ma’aikatan gwamnati.
Daurawa ya kuma buƙaci Hukumar KAROTA da ta karrama jami’in saboda nuna ƙwarewa, riƙon amana da kuma ƙin amincewa da cin hanci.