Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar da shirin kai farmaki a Nijeriya bayan umarnin tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, bisa zargin kisan Kiristoci a arewacin ƙasar kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Rahoton ya nuna an tsara matakai uku wato mai nauyi, matsakaici da mai sauƙi domin bai wa gwamnati damar zabar irin martanin da ya dace ta ɗauka.

Shirin mai nauyi ya haɗa da tura jiragen yaƙi zuwa tekun Guinea don kai hare-hare a Arewacin Nijeriya, yayin da matsakaicin mataki zai dogara da jirage marasa matuka wajen kai farmaki kan sansanonin ’yan ta’adda.
Matakin na uku mai sauƙi kuma zai kasance haɗin gwiwa da sojojin Nijeriya domin yakar Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta’addanci, tare da kare fararen hula a yankin.