Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai na farko tun kafuwarta, inda ta yaye ɗalibai 177 daga sassan kimiyya da ilimin zamantakewa.
Shugaban jami’ar, Farfesa Adamu Idris Tanko, ya bayyana cewa ɗalibai 22 sun samu First Class wato daraja ta daya da ɗalibai 57 suka samu daraja ta biyu wato Second Class Upper da 65 suka samu Second Class Lower sai ɗalibai 32 suka samu Third Class, yayin da ɗaya ya samu makin tsallakewa.
Fitattun dalibai biyu mata, Amina Anna Kabir da Nwachukwu Esther Kelechi, sun samu CGPA na 4.97 daga 5.00, kuma mata ne 19 daga cikin waɗanda suka samu First Class.

Farfesa Tanko ya ce wasu daga cikinsu za a ɗauke su aiki a matsayin kananan Malamai.
Rundunar Sojin Amuruka ta kammala tsara yadda za ta kawo wa Nigeria hari
Haka kuma, jami’ar ta bai wa fitaccen malamin Alƙur’ani, Ustaz Ahmad Sulaiman Ibrahim, digirin girmamawa na Doctor of Letters (Honoris Causa) saboda gudummawar sa ga ilimin addini.
Bikin ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da malamai da ‘yan kasuwa, inda aka yaba da ci gaban jami’ar wajen samar da ɗalibai masu nagarta da ƙwarewa.