Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga ƴan Najeriya su kwantar da hankulansu, yana mai cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakan da suka dace don tabbatar da ingantuwar tsaron rayuka da dukiyoyinsu.
Yayin isar da saƙon shugaban ƙasar, jim kaɗan bayan ganawa da shi, ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris, ya ce shugaban na yin duk mai yiwuwa domin inganta tsaro a ƙasar.
”Mun tattauna batun barazanar da Trump ya yi wa ƙasarmu, kuma shugaban ƙasa na nazarin barazanar cikin tsanaki, inda yake ƙoƙarin fahimtar da ƙasashen duniya irin ƙoƙarin da ƙasarsa ke yi wajen magance matsalar tsaron ƙasar”, in ji shi.

Cikin wani bidiyon hirar ministan da gidan talbijin na ƙasar, NTA ya wallafa , ministan ya ce ko sauya shugabannin tsaron da Tinubu ya yi a makonni biyu da suka gabata na da nasaba da ingantuwar tsaron ƙasar.
”Bayyana Najeriya da ƙasar ba a girmama addini, ba daidai ba ne, kundin tsarin mulkinmu ya yi tanadin cewa kowa na da damar yin addininsa ba tare da tsangwama ba”, in ji shi.
Ya ƙara da cewa ”shugaban na nan yana nazarin waɗannan abubuwa cikin tsanaki, kuma da yardar Allah wanna abu zai wuce”.