Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce zai ci gaba da harkokin siyasa har zuwa lokacin da zai bar duniya.
Malam Shekarau ya bayyana hakan ne yayain taron manema labarai da ya kira a gidan sa a wani bangare na bikin cikar sa shekaru 70 da haihuwa.

Shekarau ya ce wajibi ne ɗan adam ya shiga harkar siyasa don kawo canji mai kyau.
A cewar Shekarau, shiga siyasa lamari ne da zai baiwa dan adam dama ya bada gudunmawar da wajen taimakawa al’umma, inda ya ce burin da a duniya shine taimakon al’umma.
Shekarau ya kara da cewa ya kamata dai mutum ya shiga siyasa da kyakkyawar niyya, inda ya ce shi ya sha fada cewa ya na kula da addinin sa na Musulunci a harkokin siyasar sa.