Maikwatashi: Tsohon kwamishinan Ilimi ya rubutawa gwamnan Kano budaddiyar Wasika

Date:

Tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Alhaji Muhammad Sanusi S. Kiru, ya bayyana damuwarsa kan yadda aka gudanar da aikin mayar da makarantar Government Girls’ Secondary School (GGSS) Maikwatashi zuwa Kaura Goje, inda ya ce an yi manyan kura-kurai .

A cikin wata wasika da ya rubuta ga Gwamnan Jihar Kano, Kiru ya ce, duk da cewa ya yaba da kokarin gwamnatin jihar wajen inganta harkar ilimi, amma yadda aka gudanar da wannan aikin ba daidai ba ne.

Ya tuna cewa a lokacin da yake kwamishina, lokacin da aka yi irin wannan sauyi a makarantar Jido Primary School, sai da aka gina sabuwar makarantar gaba ɗaya, aka samar da kayan aiki da kujeru, kafin a mayar da ɗalibai. Wannan, a cewarsa, ya taimaka wajen kauce wa matsaloli da tsaiko ga karatun yaran.

FB IMG 1753738820016
Talla

“Abin takaici, ba a yi Irin wannan tsarin a kan makarantar Maikwatashi ba. An rusa tsohuwar makaranta kafin a kammala sabuwar, abin da ya janyo wa ɗalibai, malamai da al’umma wahala da rudani,” in ji shi.

Kiru ya ce masu kula da aikin sun nuna rashin kwarewa da sanin Makaman aiki wajen tafiyar da irin wannan tsarin mai sarkakiya.

Haka kuma, tsohon kwamishinan ya bayyana rashin jin daɗinsa kan hujjojin da aka bayar wajen tashin Makarantar ta maikwatashi, musamman yadda aka nuna al’ummar Sabon Gari a matsayin masu laifi da ’yan daba. Ya ce wannan kalami bai dace ba, musamman la’akari da irin gudunmawar da wannan al’umma su ke bayarwa ga ci gaban jihar, da kuma yadda za ka taka rawa wajen zuwan Wannan gwamnatin a zaben 2023.

Gwamnatin Kano ta sauyawa makarantar mata ta Mai Kwatashi matsugunni

Kiru ya kuma bayyana damuwarsa kan labarin cewa filin tsohuwar makarantar ana sayar da shi ne kan naira miliyan ɗari (₦100,000,000) kowanne fuloti, yana mai cewa da wannan da gwamnatin ta mayar da wurin zuwa filin wasanni, dakin taro ko wani abu da al’umma za su amfana.

Ya kuma soki maganganun da mai baiwa gwamnan kano shawara na musamman kan harkokin siyasa, Sunusi Surajo Kwankwaso, ya yi a cikin wani faifan bidiyo , yana cewa bai kamata wanda ba shi da ruwa da tsaki a harkar ilimi ya rika magana kan irin wannan batu ba.

Tsohon kwamishinan ya yabawa kwamishinan ilimi na yanzu bisa yadda ya guji tsoma ma’aikatarsa cikin rikicin, yana mai cewa har yanzu akwai damar gyara kura-kuran da aka tafka.

A karshe, Kiru ya bukaci gwamnati ta dauki darasi daga wannan al’amari, domin ta inganta tsarin kula da harkokin ilimi a jihar cikin gaskiya, tsari, da tuntubar masu ruwa da tsaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta sauyawa makarantar mata ta Mai Kwatashi matsugunni

Ma'aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta ɗauke Karantar Sakandare...

Sule Lamido, Ya Yi Barazanar Maka Shugabannin PDP a Kotu

  Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana...

Tsofaffin Kansiloli Sun Yi Saukar Alƙur’ani da Addu’a na Musamman ga Gwamna Abba

  Ƙungiyar tsofaffin kansiloli na jihar Kano ta gudanar da...

Hisbah ta kama mutane 25 bisa zargin shirya auren jinsi a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama akalla mutane...