Rundunar yansanda ta Kasa reshen jihar Kano ta ce ta yi nasarar kama wasu da take zargin yanbindiga ne masu satar mutane domin kudin fansa.
Rundunar yansandan ta ce ta kama mutum biyu a ranar Asabar a yankin Shanono bayan samun bayanan sirri.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa Jami’in hulda da jama’a na rundunar yansandan jihar Kano ya shaida wa BBC cewa yanbindigar sun shigo ne daga jihar Katsina da ke makwabtaka da Kano.
Wannan na zuwa bayan mazauna yankin ƙaramar hukumar Shanono a jihar Kano sun koka game da yadda ‘yanbindiga masu satar mutane suka fara addabarsu suna satar mutane da kuma dabbobi.
SP Kiyawa ya tabbatar da cewa an samu kutsen wasu da ake zargin ƴanbindiga ne a yankin ƙaramar hukumar Shanono kuma suna satar mutane da dabbobinsu.