Rikici a Bebeji: Jigon Kwankwasiyya na zargin an shirya cire sunayen tsoffin kansiloli domin yin kashe-muraba

Date:

Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya a karamar hukumar Bebeji ya zargi wasu jami’an gwamnati da yunkurin cire sunayen tsoffin kansiloli daga jerin wadanda gwamnati ta shirya biya hakkokinsu, domin yin abin da ya kira da “kashe-mu-raba.”

Tsohon mataimakin shugaban majalisar kansiloli na karamar hukumar Bebeji, Hon. Yusuf Salisu Baguda, ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai.

Ya ce akwai wasu mutane da ke kokarin saka sunayen wadanda ba kansiloli ba cikin jerin wadanda za a biya.

“Akwai wani jami’in gwamnatinmu ta Kwankwasiyya da mu ke zargin yana da hannu wajen shirya cire sunayen tsoffin kansiloli na gaske da suka yi aiki daga shekarar 2018 zuwa 2021, domin a saka wasu sabbi da ba su da alaka da majalisar, da nufin raba kudaden da Gwamnan Kano zai tura musu,” in ji Baguda.

Baguda ya roki Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya duba lamarin da idon basira, yana mai cewa akwai zargi mai karfi da ke bukatar a gudanar da cikakken bincike don tabbatar da gaskiya.

“Muna kira ga Mai Girma Gwamna da ya sa ido a wannan lamari. Akwai abin da ke faruwa a Karamar Hukumar Bebeji da ya kamata a bincika sosai,” in ji shi.

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito cewa a kwanakin baya gwamnan Kano ya ɗauki gabarar biyan hakkokin tsofaffin Kansilolin da suka yi aiki da tsohuwar gwamnatin da ta gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

KANFEST 2025: Gwamna Abba ya umarci sarakunan Kano da su ci gaba da hawan sallah

  Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya umarci...

Gidauniyar Pyramid of Heart sun kai tallafin na’urar Oxygen Concentrated Asibitin Murtala dake Kano

Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhd dake Kano ya yabawa...

Da dumi-dumi: ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta dakatar da...

Ba mu da wata matsala da Ofishin mataimakin shugaban Kasa – NAHCON

Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta karyata wani rahoto...